Isa ga babban shafi
Premier League

Wenger ya mayar wa Scholes da martani

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya mayar wa Paul Scholes tsohon dan wasan Manchester United da martani bayan ya fito a Telebijin yana caccakar Arsenal. Scholes yace kofin Premier ya yi wa Arsenal nisa a bana musamman a ‘yan kwanakin nan da ‘yan wasan Gunners ba su sha da dadi ba.

Arsene Wenger, kocin Arsenal
Arsene Wenger, kocin Arsenal
Talla

Paul Scholes yace Arsenal tana bukatar jagora, sannan ‘yan wasan tsakaiyar kungiyar suna bukatar horo da ladabi.

Amma Wenger ya mayar masa da martani yana mai cewa ya samu baraka ne saboda ‘yan wasan shi da ke jinya da suka hada da Theo Walcott da Jack Wilshere da Aaron Ramsey.

Wenger ya bugi kirji yace har yanzu yana da yakinin lashe Premier a bana, duk da ya kwashe shekaru 9 ba kofi.

A karshen makon nan Arsenal da Manchester City za su sake karawa, Wanda babban kalubale ne akan Arsenal bayan ta sha kashi a hannun Chelsea ci 6-0 a dai dai lokacin da Arsene Wenger ke yin haskawa karo na 1,000 a mastayin kocin Arsenal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.