Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

An tsare shugaban Club din al-Ahly na Masar a gidan kaso

An kama tare da daure shugaban Club din al-Ahly na kasar Masar Hassan Hamdi akan zarginsa da aikata laifukan da suka shafi cin Hanci da Rashawa

Hassan Hamdi
Hassan Hamdi
Talla

A ranar Lahadi ne aka kama Hamdi kuma an ce zai ci gaba da zama a Daure har tsawon kwanaki 15 domin hana shi fita kasar Masar har sai an kammala bincike akansa.

A shekarar 1949 ne aka haifi Hassan Hamdi kuma shi ne na 13 daga cikin mutanen da suka yi shugabancin wannan Kungiyar wasar kwallon Kafa ta Masar, kuma shi ne babban shugaban babban Kamfanin tallata Haja na al-Ahram da ke a kasar Masar.

Al Ahly ce kadai Kungiyar da ya yi bugawa wasa a baya wato a cikin shekarun 1969 zuwa 1978, kuma a haka har ya dare matsayin shugaban Kungiyar a 2007 bayan mutuwar tsohon shugaban Kungiyar Saleh Salim.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.