Isa ga babban shafi
Champions League

Moyes na Manchester ya daurawa kansa laifi

Mai horar da ‘Yan wasan Manchester United David Moyes ya daura wa kansa laifin kashin da suka sha a hannun Olympiacos ta Girka a gasar zakarun Turai a jiya Talata. Wannan shi ne ya kara fito da barakar da ke tattare da Manchester United a bana bayan ta sha kashi ci 2-0.

David Moyes, na Manchester United
David Moyes, na Manchester United
Talla

Tun kafin wasan, ana ganin Manchester ta samu bagas saboda an hada kungiyar wasa da Olympiacos.

David Moyes wanda ya gaji Sir Alex Ferguson yace wannan shi ne wasan shi mafi muni a Turai, kuma yanzu akwai babban kalubale a gaban shi domin rama kwallayen da Olympiacos ta zira a ragar United.

A Tarihi dai, rabon United ta rama irin wannan dukan an kwashe tsawon shekaru 30, a lokacin da suka lallasa Barcelona ci 3-0 a filin wasa na Old Trafford.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.