Isa ga babban shafi

Macron ya roki manyan kasashe su kara yawan tallafinsu ga Ukraine

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci abokan huldar Ukraine da su sabunta tare da kara yawan tallafin da suke bai wa Ukraine akan yakin da take gwabzawa da Rasha.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa yayin jawabinsa a taron taimakawa Ukraine da ya karbi bakonci a Paris.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa yayin jawabinsa a taron taimakawa Ukraine da ya karbi bakonci a Paris. AP - Gonzalo Fuentes
Talla

Macron ya yi wannan kira ne bayan bude taron kasashen yammacin Turai a birnin Paris don taimaka wa Ukraine, shekaru biyu bayan yakin da Rasha ta kaddamar kanta.

Shugabannin kasashen Turai sama da 25 ne ke halartar taron na birnin Paris, inda shugaba Macron ya koka kan yadda sojojin Ukraine suka fara sarewa a fagen daga, a dai dai lokacin da takwarorinsu na Rasha suka zafafa hare-hare, tare da shirya kaddamar da karin wasu, lamarin da ya ce ko shakkah babu zai girgiza ‘yan kasar ta Ukraine.

Masu sharhi dai na kallon karbar bakuncin taron na kasa da kasa da shugaban na Faransa ke yi a matsyin dama gare shi da zai yi amfani da ita wajen bayyana kansa a matsayin sabon jagoran kasashen yammacin Turai, musamman dangane da kokarin dakile aniyar Rasha kan Ukraine, a dai dai lokacin da suke fargabar akwai yiwuwar nan gaba Amurka za ta janye tallafin makudan kudi da makaman da ta ke bai wa kasar ta Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.