Isa ga babban shafi

Duniya na fuskantar barazana matukar Trump ya lashe zaben Amurka- NATO

Shugaban kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg, ya yi gargadi game da kalaman tsohon shugaban Amurka Donald Trump, inda ya ce duk wani matakin da za a dauka da zai sanya kungiyar ta kasa kare kanta, babbar barazana ce ga tsaronsu dama Amurka.

Jens Stoltenberg em coletiva de imprensa em Bruxelas na última semana. (07/01/2024)
Jens Stoltenberg em coletiva de imprensa em Bruxelas na última semana. (07/01/2024) AP - Virginia Mayo
Talla

A ranar asabar da ta gabata ne dai Trump da ke jawabi a wajen gangamin sake zabensa, ya ce ba zai bai wa duk wata mambar kungiyar NATO da ba ta iya biyan kudadenta kari ba, lamarin da ake ganin a matsayin karfafawa Rasha gwiwa wajen kai musu hari.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da tsohon shugaban na Amurka, ke yin irin wannan barazana ga kawancan kungiyar, kan rashin iya samar da kudaden da ta ke bukata wajen gudanar da ayyukanta.

Tuni dai shugaban Majalisar Tarayyar Turai Charles Michel, ya bulla a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter ya na mai watsi da kalaman Trump da ya bayyanasu a matsayin marasa amfani.

Ya ce kalaman ba komai bane face kara karfafa wa Putin gwiwa da kuma kawo rashin zaman lafiya a duniya baki daya.

Shugaban NATO Stoltenberg ya ce idan har Amurka ta dauki wancan mataki, hakan zai jefa sojojin Turai da na Amurka cikin hatsari, don haka ya ce ya na fatan duk wanda ya lashe zaben Amurka, kasar ta ci gaba da bai wa NATO goyon bayan da ya kamata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.