Isa ga babban shafi

Adadin wadanda suka mutu a harin Rasha kan Ukraine ya zarta 30

Adadin wadanda mummunan harin Russia a Ukraine ya kasha ya kai 31 kawo yanzu kamar yadda mahukuntan kasar suka tabbatarwa da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP.

Shugaban Rasha Vladmir Putin
Shugaban Rasha Vladmir Putin AP - Alexander Zemlianichenko
Talla

 

Bayanai sun nuna cewa a jiya kadai Russia ta jefa makamai masu linzami guda 122 kan sassan Kyiv, abinda ke zama hari mafi muni da kasar ta kaiwa Ukraine tun bayan fara yakin shekaru 2 da suka gabata.

Ko da yake yiwa manema labarai jawabi kakakin rundunar sojin samar Ukraine Yuriy Ignat, ya ce akwai mamaki yadda Russia ta sami wannan nasara kasancewar na’urorin su basu nuna musu wata alama da ke nuna za’a kai hari ta sama ba.

A cewar sa a hakan ma jami’an su sun yi nasarar dakatar da wasu 87 cikin na’urori kusan 200 da Russia ta harba a yau kadai.

Bayan wannan mummunan hari ne kuma Burtaniya ta sanar da baiwa Ukraine karin tallafin makamai masu linzami guda 200, wadanda zata yi amfani da su wajen kare kanta daga hare-haren Rasha.

Sai dai kuma jim kadan bayan wannan alkawari shugaban Rasha Vladmir Putin ya ce babu wata barzana da kasashen yammaci zasu yi masa kan ya saurarawa Ukraine, don haka hare-hare zafafa yanzu Ukraine ta fara gani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.