Isa ga babban shafi

Jamus na shirin baiwa jama'a damar busa tabar wiwi don samun nishadi

Gwamnatin Jamus ta amince da shirin bai wa 'yan kasar damar zukar tabar wiwi don nishadi, yayin da 'yan adawar kasar da alkalai ke caccakar wannan matakin.

Jamusawa sun samu damar shan wiwi ba tare da fuskantar hukunci ba.
Jamusawa sun samu damar shan wiwi ba tare da fuskantar hukunci ba. AFP/File
Talla

Wannan kudurin doka na bukatar sahalewar majalisa kafin bai wa mutane ‘yan sama da shekaru 18 damar mallaka ko kuma busa tabar wiwin da yawanta bai wuce giram 25 ba.

Kunshin dokar ya bai wa jama’a damar shuka tabar wiwin da ba ta wuce tushe uku ba, ma’ana dai iya wadda mutum zai iya busawa don samun nishadi.

Idan har wannan doka ta sami damar sahalewar majalisa, za ta bai wa jama’a damar kafa kungiyoyin mashaya wiwin da mambobinsu ba su wuce 500 ba, kuma cikin wannan kungiya suna da damar shukawa, cinikayya, safara da kuma kunna mata wuta a duk lokacin da suka so.

Kodayake mayar da martani, Ministan Lafiyar Kasar Karl Lauterbach ya ce wannan ba karamin ci gaba ne da kasar ta samu ba, kuma zai bai wa mashayan damar wartsakewa da ragewa kwakwalensu lodin damuwar da ta dabaibaye su.

A watan Afrilun badi ne, ake sa ran fara bada lasisin wannan sabuwar doka da ke zama banbarakwai a idanun jama'a da yawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.