Isa ga babban shafi

Erdogan ya goyi bayan zaman Ukraine mamba a kungiyar tsaro ta NATO

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya nuna goyon baya ga Ukraine na shiga kungiyar NATO, sai dai kuma ya bukaci a koma kan teburin sulhu don samar da zaman lafiya ta hanyar kawo karshen rikicin da ya barke tsakanin Rasha da Ukraine.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya nuna goyon baya ga Ukraine na shiga kungiyar NATO.
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya nuna goyon baya ga Ukraine na shiga kungiyar NATO. via REUTERS - MURAT CETINMUHURDAR/PPO
Talla

A lokacin wani taron manane labarai na hadin gwiwa da suka gudanar a birnin Istanbul, bayan ziyarar da shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya kai masa, Erdogan ya ce ta hanyar sulhu babu wanda za a ce ya yi rashin nasara a tsakanin bangarorin.

A nasa jawabin, shugaba Zelenskyy ya godewa Erdogan bi sa goyon bayan da ya baiwa kasarsa, wanda ke zuwa gabanin taron kungiyar tsaro ta NATO da zai fara a ranar a ranar Talata a birnin Vilnius na kasar Lithuania.

Shugaban na Ukraine na ta kamun kafa na ganin an baiwa kasarsa da ke fama da rikici damar shiga kungiyar ta NATO, ya na mai cewa Ukraine ta zama kasa ta karshe da ke kare Turai daga barazanar Rasha.

A wannan makon Zelenskyy ya ziyarci kasashen Czech da Slovakia da kuma Bulgaria, domin samun goyon baya su a yukurin Ukraine na zama mamba a kungiyar ta NATO, gabanin taronta da za ta gudanar a ranakun 11 zuwa 12 ga wannan watan na Yuli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.