Isa ga babban shafi

Sarkin Holland ya nemi afuwa a game da cinikin bayi

Sarkin Willem-Alexander na Holland ya nemi afuwa  agame da hannu da kasarsa ke da shi a cinikin bayi, yana mai cewa yana ji har cikin zuciyarsa cewa abin ya shafe shi.

Sarki Willem-Alexander na Holland da mai dakinsa.
Sarki Willem-Alexander na Holland da mai dakinsa. REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Jawabin da ya yi a gaban tsason bayi daga yankin Suriname na  kudancin Amurka, da Tsibiran Caribean da Aruba, Bonaire da Curacao ya samu tarba mai armashi, amma wasu  da dama na cewa kamata ya yi kasar Holland ta biya diyya.

Sarkin ya bayyana a jawabin da aka watsa a kafar talabijin cewa, bauta da cinikin bayi ya nuna rashin adalci karara a wancan lokaci da doka ta sahale dillancin ‘yan adam.

Wasu da  sarkin ya yi wannan jawabi a gabansu sun ce sun yafe masa, tun da ya nemi afuwa.

Tun da aka fara batun rajin martaba rayukan bakaken fata a Amurka, wato Black Lives Matter, Netherlands ta tsinci kanta a cikin wata  muhawwara maai matukar wahala a game da cinikin bayin da ta yi a zamanin da ta yi mulkin mallaka, wanda ya sa ta zama daya daga cikin kasashe masu arziki a duniya.

Sakamakon wani bincike da aka fitar a watan Yuni ya nuna cewa gidan sarautar Holland ya samu Yuro miliyan 545 daga cinikin bayi a tsakanin shekarun 1675 da 1770.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.