Isa ga babban shafi

Zelensky ya dage kan kafa kotu ta musamman don hukunta Putin

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky wanda ke ziyara a Hague, ya jaddada bukatar ganin an kafa kotu ta musamman da zata dorawa Rasha alhakin laifukan yaki.

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy yayin ziyara a kotun duniya ICC dake birnin Heague.04/05/23
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy yayin ziyara a kotun duniya ICC dake birnin Heague.04/05/23 AP - Yves Herman
Talla

Shugaba Zelensky da ke shaidawa jami'an diflomasiyya da ma’aikatan kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC wadda ta bayar da sammacin kama Vladimir Putin na Rasha bisa zargin aikata laifukan yaki yace dole a tabbatar da wanda ya aikata laifi, kuma kotu ce kadai ke da wannan hurumi.

Ukraine na neman a kafa wata kotu ta musamman da za ta tuhumi Rasha kan aikata laifukan ta'addanci saboda tana ganin hakan a matsayin wata hanya ta tabbatar da adalci kan kutse da aka musu da kuma gaggauta soma kama manyan jami'an fadar Kremlin.

Kotun ta ICC mai hedkwata a birnin Hague a halin yanzu tana gudanar da bincike kan yiwuwar an aikata laifukan yaki da cin zarafin bil adama a yakin Ukraine to amma ba ta da hurumin bin diddigi manyan laifuka na wuce gona da iri.

Wasu daga cikin masu goyon bayan Kyiv na yammacin Turai na ganin zai yi wuya a iya samun goyon bayan sauran kasashen duniya wajen kafa kotu ta musamman kan wannan batu, sai dai abin da ya fi dacewa ita ce kafa wata kotun karkashin dokar Ukraine.Amma Zelensky ya ki amincewa da ra'ayin wanan ra’ayi.

Rasha dai ta sha musanta duk wani zargin aikata cin zarafi ko laifukan yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.