Isa ga babban shafi
Mata-Maita

Scotland ta nemi yafiyar kisan Mata dubu 2 da 500 kan zargin maita

Gwamnatin kasar Scotland ta nemi gafarar iyalan wasu mata sama da dubu 2 da 500 da aka kashe saboda zargin da ake musu cewar mayu ne tsakanin karni na 16 zuwa na 18.

A wancan zamani akan yi amfani da wuta wajen kone matan da aka samu da laifin maita.
A wancan zamani akan yi amfani da wuta wajen kone matan da aka samu da laifin maita. © scot
Talla

Wannan neman gafarar ta zo ne a dai dai lokacin da ake bikin ranar mata ta duniya, inda gwamnatin ta mika sakon neman gafara ga kungiyar da ake kira ‘Witches of Scotland’ wadda ta dade ta na bukatar ganin an bi hakkin wadannan mata sama da 4,000 da aka yiwa irin wannan zargi.

Rahotanni sun ce akalla mutane sama da dubu 2 da 500 aka aiwatarwa hukuncin kisan, kuma kashi 4 bisa 5 daga cikin su mata ne, inda aka dinga murde wuyansu ana kona su, bayan an azabtar da su domin amsa tuhumar da ake musu.

Babbar ministar da ke kula da Scotland Nicola Sturgeon ta bayyana kisan a matsayin rashin adalci na karshe wanda ya taso sakamakon nuna wariya da kuma kyamar mata.

Sturgeon ta ce an samu wannan zaluncin ne lokacin da ba a barin mace ta zama shaida a kotu, yayinda ake yi wa wasu daga cikinsu shari’a ana kashe su saboda su talakawa ne ko kuma don kasancewarsu mata.

Ministar ta bayyana amincewar ta da aika aikan da aka yi wajen nuna rashin adalci domin mika sakon neman gafara ga wadanda da aka kashe a karkashin dokar da aka yi amfani da ita mai lamba 1563.

Rahotanni sun ce wannan matsalar ta yi kamari ne lokacin mulkin King James na 4 a Scotland wanda ya zama Sarkin Ingila a shekarar 1603 da akafi sani da King James na 1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.