Isa ga babban shafi
Netherlands

Netherlands za ta koma karkashin dokar kulle yayin bikin Kirsimeti

Firaministan Netherlands Mark Rutte, ya ce kasar za ta koma karkashin dokar kulle a lokacin bukukuwan Kirsimeti domin dakile yaduwar sabon nau’in cutar Korona na Omicron.

Firaministan kasar Netherlands Mark Rutte.
Firaministan kasar Netherlands Mark Rutte. Olivier HOSLET POOL/AFP/File
Talla

Yayin sanar da matakin, shugaba Firaministan, ya ce daga yau Lahadi, dole ne a rufe dukkanin shagunan da ba su da mahimmanci, da gidajen cin abinci, da mashaya, da Sinima, da kuma gidajen tarihi, har zuwa 14 ga watan Janairu, yayin da kuma makarantu za su rufe har zuwa akalla ranar 9 ga watan na Janairu.

Zalika an rage adadin mutanen da aka baiwa damar ziyartar iyalai a gidajensu daga 4 zuwa 2, sai dai kawai a ranar Kirsimeti 25 ga watan Disamba kawai iyalan za sui ya karbar bakuncin fiye da mutane 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.