Isa ga babban shafi
Turai-Covid-19

An gudanar da zanga-zangar adawa da matakan dakile Korona a Turai

Dubban mutane ne suka bazama tituna a nahiyar Turai da Australia don nuna rashin amincewarsu da sabbin matakin da hukumomi ke dauka don dakile anobar Covid-19 ke sake kunno kai.

Masu zanga zanga a Australia.
Masu zanga zanga a Australia. William WEST AFP
Talla

Rikici ya barke bayan kwana guda da zanga zangar lumana a kasar Netherlands, inda masu zanga zangar suka yi ta jifan ‘yan sanda da duwatsu da tirtsitsin wuta tare da kona kekuna, lamarin da ya sa aka kama da dama daga cikinsu.

Nahiyar Turai na fama da sake bullar annobar Covid-19 kuma kasashe da dama sun tsaurara matakan kariya, inda a Juma’a Austria ta sanar da ‘yar kwaryakwaryar dokar kulle.

A Asabar Netherlands ta sanar da kwaryakwaryar dokar kulle, kuma tana shirin hana wadanda ba su yi rigakafi ba shiga kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.