Isa ga babban shafi
Faransa - Amurka

Macron da Harris sun cimma matsaya kan gayara alakar Faransa da Amurka

Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris da shugaban Faransa Emmanuel Macron, sun cimma matsaya kan gayara alakar kasashensu, bayan tsamin da dangantakarsu ta yi, akan kwangilar ginawa kasar Australia jiragen yakin karkashin ruwa.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris a birnin Paris, 10 ga Nuwamba, 2021.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris a birnin Paris, 10 ga Nuwamba, 2021. AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

Macron ya fusata ne a watan Satumba lokacin da Australia ta juyawa Faransa baya kan yarjejeniyar gina musu jiragen yakin na karkashin teku, inda ya koma ga Amurka, yarjejeniyar da aka cimma a asirce.

Bayan da aka shafe makwanni da fusatar da Faransa tayi ne kuma da fari shugaba Emmanuel Macron ya gana da takwaransa na Amurka Joe Biden a birnin Rome, ranar 29 ga watan Oktoba, kafin daga bisani a jiya Macron din ya gana da mataimkiyar Biden wato Kamala Harris a fadar Elysee dake birnin Paris, inda ta shafe kwanaki 4 tana ziyara domin maido da kyakkyawar dangantaka tsakaninsu.

Baya ga karfafa huldar difomasiyya tsakaninsu, manyan batutuwan da shugaba Macron da kuma Harris suka tattauna akai dai sun hada da "hadin gwiwa wajen tunkarar yaki da matsalar sauyin yanayi, da kuma rage tasirin kasar China yankin tekun India da Pacific, lamarin dake tayar da hankalin kasashen Turai da Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.