Isa ga babban shafi
Australia

Australia ta kafa asusun dala biliyan 738 don yaki da dumamar yanayi

Fira Ministan Australia Scott Morrison, ya kaddamar da asusun saka hannun jari na dalar Australia biliyan 738 don hanzarta fara aiwatar da sabbin fasahohin rage fitar da hayaki mai guba, da kuma fara adana iskar ta carbon, domin gwamnatinsa ta cimma muradun yaki da matsalar dumamar yanayi.

Wata masana'antar sarrafa sinadarai a kusa da Sydney babban birnin kasar Australia.
Wata masana'antar sarrafa sinadarai a kusa da Sydney babban birnin kasar Australia. © REUTERS/David Gray/File Photo
Talla

Sabon yunkurin Fira Ministan na Australia na zuwa ne a yayin da ya rage watanni kalilan a yi babban zaben kasar.

Bayan kaddamar da gidauniyar, Morrison ya bayyana fatan kamfanoni masu zaman kansu su ba da tasu gudunmawar da za ta kai akalla dalar Australia miliyan 500 ga asusun.

 Sabuwar manufar gwamnatin Australia ta neman rage hayakin Carbon da ake fitarwa a kasar ya zo ne bayan da Fira Minista Morrison ya sha suka sosai a taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi a birnin Glasgow dake Scotland, saboda gazawar da ya yi wajen tsara cimma muradun rage matsalar sauyin yanayi nan da shekarar 2030.

A halin yanzu dai Autralia na da burin rage fitar da hayaki da kashi 26 ta yadda zai koma zuwa kashi 28 cikin 100, a kasa da matakin da ta rika fitarwa a shekarar 2005.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.