An yi zanga-zanga a Glasgow gabannin fara taro kan dumamar yanayi
Daruruwan masu fafutuka sun yi zanga-zanga a Glasgow babban birnin Scotland domin kira ga shugabannin duniya da su gaggauta daukar matakan dakile matsalar sauyin yanayi.
Wallafawa ranar:
Zanga-zangar dai itace irinta mafi girma da aka yi a birnin Scotland gabanin muhimmin taron kasashen duniya kan matsalar.
Bayanai sun ce mahalarta zanga-zangar sun yiwo tattaki ne daga yankuna na nesa ciki har da wasu kasashen Turai, abinda ya sa wasunsu yin tafiya mai nisa domin bayyana takaicinsu ga taron da Majalisar Dinkin Duniya za ta fara jagoranta daga ranar Lahadin nan har zuwa ranar 12 ga watan Nuwamba.
Masu zanga-zangar da suka yi tattaki a tsakiyar Glasgow babban birnin Scotland rike da kwalaye masu dauke da kalaman "ayyuka muke bukata ba kalmomi ba".
Mambobin kungiyar rajin kare muhalli ta ‘Extinction Rebellion’ ne suka jagoranci gangamin da ya gudana, wadanda suka yi fice ya kawo tsaiko ga biranen duniya akan manufarsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu