Isa ga babban shafi
Faransa-Australia

Shugabannin Faransa, Australia sun gana a karon farko bayan sabani

A karon farko shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tattauna da Firaministan Australia Scott Marrison ta wayar tarho game da rikicin diflomasiyar kasashen biyu da ya barke sakamakon soke wata yarjejeniyar cinikayyar jiragen yakin karkashin teku.

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron. REUTERS - POOL
Talla

A cikin wata sanarwa da fadar gwamnatin Faransa ta  Elysee ta fitar, shugaba Macron ya jaddada cewa, matakin da Australia ta dauka na soke yarjejeniyar, ya amfanar da Amurka ne, lamarin da ya tsinka igiyar amintaka da ke tsakanin kasaashen biyu.

Macron ya kara da cewa, yanzu ya rage wa gwamnatin Australia da ta gabatar da kwakkwaran matakin da zai kunshi kudurin hukumomin kasar na sake sabunta alaka tsakaninsu da Faransa .

Gwamnatin Faransa dai, ta fusata matuka bayan Australia ta yi watsi da yarjejeniyar a watan jiya ba tare da fara gabatar da wani gargadi ba, inda ta yi gaban kanta wajen cimma  wata sabuwar  yarjejeniyar tsaro ta  daban da Amurka da Birtaniya.

A shekarar 2016 ne, Australia ta rattaba hannu kan yarjejeniyar sayen jiragen yakin karkashin teku daga Faransa kan kudin da ya kai Euro biliyan 31 a wancan lokaci.

Jim kadan da samun sabani a tsakanin kasashen biyu, Faransa ta janye jakadanta daga Australia da Amurka domin nuna bacin ranta , inda Firaminisrtan Harkokin Wajen kasar, Jean-Yves Le Drian ya ce, an ci amanarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.