Isa ga babban shafi
Ambaliya - Turai

Adadin mutanen da suka mutu dalilin ambaliyar ruwa a Turai na karuwa

An aike da sojoji da karin jami’an ceto zuwa sassan kasashen Turai a yau Asabar don taimaka wa mazauna kauyukan da mummunar ambaliyar ruwa afkawa a yammacin Turai, yanayi mafi muni da aka gani cikin shekaru da dama.

Wannan hoto da gwamnatin gundumar Cologne ta fitar ranar Juma'a, 16 ga watan Yulin, 2021, na nuna yadda mabaliyar ruwa ta yi barna a gundumar Blessem ta Erftstadt a Jamus.
Wannan hoto da gwamnatin gundumar Cologne ta fitar ranar Juma'a, 16 ga watan Yulin, 2021, na nuna yadda mabaliyar ruwa ta yi barna a gundumar Blessem ta Erftstadt a Jamus. © AP - Rhein-Erft-Kreis
Talla

Yanzu haka dai jami’an ceto sun tabbatar da karuwar adadin mutanen da suka mutu dalilin ambaliyar daga 128 zuwa 153, yayin da kuma ake ci gaba da laluben wasu mutanen da dama da suka bace.

Yadda ambaliyar ruwa ta mamaye tashar jirgin kasa dake garin Kordel a kasar Jamus.
Yadda ambaliyar ruwa ta mamaye tashar jirgin kasa dake garin Kordel a kasar Jamus. AFP - SEBASTIAN SCHMITT

Yammacin Jamus ne yankin da ambaliyar ruwan ta fi yi wa barna, yayin da kuma ta tagayyara wasu yankunan kasashen Belgium, Luxembourg da Netherlands inda ruwa hade da laka ya mamaye tituna da gidaje gami da yanke hanyoyin isa wasu kauyuka.

A Jamus kadai mutane 133 aka tabbatar da mutuwarsu yayin da kuma masu aikin ceto suka yi gargadin adadin zai iya karuwa  sakamakon ci gaba da lalubane mutanen da suka bace cikin baraguzan ginin da ambaliyar ta rushe.

A Belgium dake mwaftaka da Jamus kuwa, alkaluman gwamnati sun tabbatar da cewa adadin wadanda suka mutu ya haura 20, yayin da wasu mutanen fiye da dubu 21,000 suka rasa wutar lantarki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.