Isa ga babban shafi
Wasanni - Coronavirus

Scotland: Mutane dubu 2 sun kamu da Korona bayan kallon wasannin Euro 2020

Hukumomin kiwon lafiya a kasar Scotland sun ce mutane kusan dubu biyu ne suka harbu da kwayar cutar Korona, sakamakon cinkoson da aka samu a wasannin kwallon kafa na Turai a kasar.

Wasu magoya bayan yankin Scotland, yayin karawar tawagar su ta kwallon kafa da Ingila a gasar cin kofin kasashen Turai ta Euro 2020.
Wasu magoya bayan yankin Scotland, yayin karawar tawagar su ta kwallon kafa da Ingila a gasar cin kofin kasashen Turai ta Euro 2020. © Reuters
Talla

Hukumar lafiyar Scotland, ta ce daga ranar 11 zuwa 28 ga watan na jiya sama da mutane dubu 32 ‘yan asalin yankin aka yi wa gwaji bayan sun kallin wasan kwallon, daga cikinsu kuma dubu 1, da 991 ne suka kamu da cutar.

Rahoton baya bayan nan kan kamuwar da mutanen suka yi da cutar Korona a Scotland ya zo ne a daidai lokacin da masu ruwa da tsaki ke tafka muhawara yadda wassanin kusa da na karshe da kuma na karshe za su gudana.

A shekarar 2020 annobar Korona ta tilastawa hukumomin kasashe haramtawa ‘yan kallo damar shiga filayen wasanni domin baiwa idanunsu abinci kai tsaye abinda ya janyowa kungiyoyi tafka hasarar kudaden shigar da suke samu ta hanyar saida tikitin shiga filyensu don kallon wasanni, baya ga ragewa wasannin armashi musamman na kwallon kafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.