Isa ga babban shafi
Jamus

Jamus na son a fara yi wa Turawa riga-kafin corona

Kasar Jamus ta bukaci Kungiyar Tarayyar Turai da ta amince da riga-kafin cutar coronavirus da kamfanonin BioNTech da Pfizer suka samar kafin bikin Kirismati.

Margaret Keenan, matar da aka fara yi wa allurar-riga-kafin corona a Birtaniya
Margaret Keenan, matar da aka fara yi wa allurar-riga-kafin corona a Birtaniya Jacob King/AP
Talla

Ministan Lafiyar Jamus, Jens Spahn ya shaida wa manema labarai a birnin Berlin cewa, muradinsu shi ne a amince da riga-kafin cutar kafin ranar bikin Kirsimati, yana mai cewa, suna son a fara yi wa Jamusawa allurar riga-kafin kafin karshen wannan shekara.

A can baya, Hukumar Kula da Magunguna ta Turai mai Cibiya a Amsterdam ta ce, ta yi shirin gudanar da wani taro na musamman a ranar 29 ga watan Disamba domin tattaunawa kan sharuddan amincewa da riga-kafin cutar.

Jinkirin wannan taro dai, ya bar nahiyar Turai a bayan wasu kasashen duniya wadanda tuni suka amincewa da allurar riaga-kafin cikin gaggawa kamar Birtaniya da Canada da Amurka da suka fara yi wa jama’arsu riga-kafin.

Kodayake Jaridar Bild ta Jamus ta rawaito cewa, Hukumar Kula da Magungunan ta Turai na son a yanzu ta gudanar da taronta a ranar 23 ga watan Disamba, abin da Ministan Lafiya na Jamus ya ce, zai zama labari mai dadi ga daukacin kasashen Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.