Isa ga babban shafi
Faransa

Kasashen Turai na cikin barazana

Shugaban yaki da ayyukan ta’addanci na Kungiyar Tarayyar Turai Gilles De Kerchove yace babu wani takamaiman mataki da za su iya dauka don kare barazanar sabbin hare hare daga mayaka masu da’awar Jihadi musamman irin hare haren ‘Yan Bindiga da aka kai a Birnin Paris na Faransa.

Shugaba Francois Hollande na Faransa da Jami'an tsaron Kasar
Shugaba Francois Hollande na Faransa da Jami'an tsaron Kasar REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Kerchove ya shaidawa da Kamfanin Dillacin Labaran Faransa cewa babu yadda za’a yi a dakile hare haren ta’adanci dari bisa dari.

Ya ce tasa keyar ‘yan kasashen Turai wadanda ke dawowa daga jihadi a Syria da Iraq zuwa gidan yari ba zai zama mafita ba don za su yi amfani da damar wajen ci gaba da aikata barna.

A ganawarsa da Ministan tsaron kasar Amurka da Canada da Birtaniya a ranar lahadin da ta gabata, Kerchove ya bayyana harin da ‘yan bindiga suka kai birnin Paris a matsayin wani babban barazana ga kasashen Turai.

Ya kuma bayyana barazanar da ke fitowa daga Mayakan IS akan za su ci gaba da kai hare-hare a kasashen duniya, kamar yadda Mayakan al-Qaeda suka yi gargadi.

A cewarsa ya zama dole kasashen Turai su tashin haikan don bijiro da hanyoyin kawo karshen ta’adanci da ke neman dabaibaiye kasashensu.

Hukumar ‘Yan Sandan kasashen Turai tace yanzu haka mutanen yankin kusan 5,000 suka shiga cikin kungiyoyin da ke da alaka da ta’addanci. Shugaban ‘Yan Sandan Rob Wainwright ne ya bayyana haka yayin da ya ke jawabi ga kwamitin tsaro na majalisar Birtaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.