Isa ga babban shafi
Ukraine-Amurka-Rasha

Za’a kai karshen rikicin kasar Ukraine

Sabon shugaban kasar Ukraine mai samun goyon bayan kassahen Turai Petro Poroshenko ya shaidawa Duniya cewar tilas fadan da ‘yan tawaye masu goyon bayan kasar Rasha a gabashin kasar ya kawo karshe a karshen Satin nan.Ya fadi hakan ne kuwa bayan da aka rantsar da shi a matsayin sabon shugaba. 

REUTERS/Shamil Zhumatov
Talla

Sabon shugaban ya ce a wurinshi babbar damuwa ce ga kowace rana aka rasa rayuka, da kuma ranar da Ukrain ta shiga hargitsi, kuma ba abu ne da ba za su yi na’am da shi ba.

A cikin wata sanarwar da ya sanya wa Hannu, shugaban ya ce ya zama wajibi su tabbatar da kai karshen fadan, kuma yin hakan dole su samar da tsaro a kan iyakokin kasar.

Kalaman na shugaban dai sun zo ne bayan wani zagayen tattaunawa da Jakadan kasar Rasha a kasar da kuma jakadan wata kungiyar samar da tsaro ta yankin kasashen Turai da ake kira [OSCE] a takaice kuma a Turance.

Fadan da ake ci gaba da tafkawa tsakanin ‘yan tawaye masu goyon bayan kasar Rasha da Dakarun kasar Ukraine dai, ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, a yayin da gamayyar Kasashen yammaci da suka kira kan su G7 bayan fitar da Rasha daga cikinsu ke ta matsawa Rasha lamba.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya gabatar da sanarwar kiran ‘yan tawayen masu goyon bayan kasar sa da su hadiye fushi bayan wata bukata da shugaban kasar Amurka barrack Obama da wasu shugabannin kasashen Turai suka gabatar masa.

Rasha dai ta lashi Takobin dakatar da baiwa yankin kasashen Turai Iskar Gas, muddin ba’a biyata dimbin bashin da take biya ba, matakin da Turai ke ganin ka iya saka su babbar matsala.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.