Isa ga babban shafi
Hungary

Jam’iyyar Orban ta yi ikirarin nasara a zaben Hungary

Jam’iyyar Firaministan kasar Hungary Viktor Orban ta yi ikirarin lashe zaben ‘yan Majalisar Dokoki da aka gudanar a kasar inda sakamakon farko na zaben ke nuni da cewa jam’iyyar mai na kan hanyar samun nasara.

Firaministan Hungary Viktor Orban a lokacin da ya kada kuri'ar zabe.
Firaministan Hungary Viktor Orban a lokacin da ya kada kuri'ar zabe. (©Reuters)
Talla

An dai samu fitowar jama’a dafifi a wannan zabe da aka gudanar a ranar Lahadi, domin samun shiga majalisar kasar mai kujeru 199.

Firaminista mai ci Viktor Orban, dan kimanin shekaru 50 a duniya, ya mallaki kashi biyu cikin uku na kujerun da ake da su a majalisar da ke daf da kawo karshen wa’adin aikinta, amma yayin da alkalumma ke nuni da cewa zai sake rinjaye a wannan zabe, masu hasashe sun ce abu ne mai wuya ya iya samun yawan kujerun da ya ke da su a tsohuwar majalisar.

A lokacin da ya ke zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya jefa kuri’arsa a birnin Budapest, Firaminista Orban, yace ba ya da wata fargaba dangane da makomarsa a fagen siyasar kasar, yayin da alkalumma ke tabbatar da cewa ita ma jam’iyyar masu tsaka-tsakan ra’ayi za ta ci gaba da kasancewa a matsayin ta biyu cikin zauren majalisar.

Hungary wadda ke gabashin Turai, ta yi fama da matsaloli na tattalin arziki na tsawon shekaru 10 lokacin da take karkashin mulkin jam’iyyar masu ra’ayin gurguzu, sai dai zuwan shugaba Viktor Orban kan karagar mulki a 2010, ya taimaka wajen tsamo kasar daga durkushewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.