Isa ga babban shafi
Lafiya Jari ce

Karancin ruwa na haddasa tarin cutuka ga al'ummar arewacin Kamaru

Wallafawa ranar:

Shirin Lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda al’ummar yankin arewacin kamaru ke fuskanta matsalar rashin tsaftatacce kuma wadataccen ruwan sha ba, wanda ke haddasa gagarumar matsala ga lafiyar mazauna yankunan, wannan shi ne maudu’in da shirin na wannan mako zai mayar da hankali akai.

Wasu mata kenan da ke neman ruwa a rijiyar burtsatse.
Wasu mata kenan da ke neman ruwa a rijiyar burtsatse. © Solidaridad
Talla

Tsaftatacce kuma wadataccen ruwan sha na  matsayin ginshikin lafiyar jama’a wanda kuma rashin ke matsayin babbar barazanar bullar tarin cutuka na cikin wajen jikin bil’ada, sai dai samun ruwan sha ko na amfani ga galibin al’ummomin da ke rayuwa a yankin arewacin Kamaru na matukar wahala.

A baya-bayan nan al’ummar yankin na ganin bullar cutuka da dama masu alaka da rashin tsaftataccen ruwan sha ko na amfani, yankin da kashi 43.5 na al’ummarsa ne kadai musamman mazauna karkara kan iya samun wadatacce kuma tsaftataccen ruwa.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shiri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.