Ana fuskantar karancin jinin tallafi a asibitocin jamhuriyyar Nijar
Wallafawa ranar:
Kunna - 10:18
Shirin Lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda wasu asibotoci a Jamhuriyyar Nijar ke fama da karancin jini sakamakon rashin masu bayar da gudunmawar jinin don tallafawa marasa lafiya.
Bayanai sun bayyana cewa galibi a irin wannan lokaci na watan Ramadana akan fuskanci irin wannan matsala ta karancin hatta a sashen 'yan haihuwa da kuma bangaren da ake kula da masu lalurar koda.
Duk da matakin da asibitoci suka dauka na adana jinin don kaucewa fuskantar yankewarsa, sai dai Bankin jini na jihar Damagaram na ganin abu ne mai wuya idan ba a sake fuskantar yankewarsa a bana ba.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin..............
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu