A cikin shirin Nishadi na wannan mako,Salissou Hamissou ya yi kokarin jin ko ya ya masu gudanar da sana'ar CD ke rayuwa ganin ta yada aka samu ci gaba a duniyar Fina-finai a wannan zamani.Banda haka ya kuma ji ta bakin wasu daga cikin mawwaka a Duniyar Hausa.
Sauran kashi-kashi
-
An sace kyautar Carosse d’Or a gidan mai shirya fina-finai Souleymane Cisse
Shekara daya kenan da fittacen mai shirya fina-finan kasar Mali darekta Souleymane Cissé ya karbi kyautar Carrosse d'Or, karramawa da aka bashi a birnin Cannes na kasar Faransa lokacin bikin baje kolli da karama masu shirya fina-finan Duniya.Darekta Souleymane Cissé na daga cikin ziratan masu shirya fina-fina a Afrika,wanda tsawon shekaru 50 ya kasance mai fada a ji a wannan masana’anta.04/05/202419:24 -
Aya Nakamura,da Gazo suka lashe kyautar mawakan shekara na Faransa
An gudanar da bikin bayar da kyaututuka ga mawakan zamani a birnin Paris na kasar Faransa, inda mawaka da suka yi fice kamar su Aya Daniocko da aka fi sani da sunan Aya Nakamura, da Ibrahim Diakite mai suna Gazo suka kasance a sahun gaba a wannan biki na mawaka a Faransa.27/04/202419:34 -
Ƙorafin Zango ya haifar da cece-kuce a ciki da wajen Kannywood
Shirin 'Dandalin Nishaɗi' na wannan mako tare da Abdoulaye Issa ya maida hankali kan wani batu da ya kare da shafukan sada zamunta wato kalaman da ɗay daga cikin jarumai a masana’antar fina-finai ta Kannywood Adam A Zango ya yi wanda ya fito tare da bayyana damuwa kan abin da ya kira butulci da aka masa, al’amarin da ya janyo martani daga da damacikin masu bibiyar masana’antar ta Kannywood. Sai kuma yadda ake shirin bikin kalankuwa na Femua da zai gudana a kasar Cote d’Ivoire.20/04/202420:12 -
Bangaren masana'antu zasu iya taimakawa wajen ci gaban tattalin arzikin Najeriya
Wannan bikin baje kolin fasaha karkashin inuwar Bankin Afirka, a karkashin sa ido da gudanarwa masana’anta da kuma wurin koyon ayuka na Soto Gallery ya shirya, yana baiwa matasa masu hazaka da fasaha damar samun horo na zamani da ya dace daga kowace kusurwa ta Najeriya.23/03/202420:10 -
Yadda jama’a ke ta bayyana ra’ayoyi kan fitar wani sabon shiri mai suna Matar Mai gari
Mai saurare a cikin shirin na wannan mako zaku ji yadda jama’a ke ta bayyana ra’ayoyi kan fitar wani sabon shiri mai suna Matar Mai gari wanda fitaciyyar jarumar fina-fina Saratu Daso ta shirya, Zamuji banbancin sa da sauran fina-finai.Akwai mu da rahoto na musamman kan mutuwar fitaccen mai wasan barkwancin nan na jamhuriyar Nijar wato Ada Mai Kano.09/03/202420:00