Dandalin Nishadi
An sace kyautar Carosse d’Or a gidan mai shirya fina-finai Souleymane Cisse
Wallafawa ranar:
Kunna - 19:24
Shekara daya kenan da fittacen mai shirya fina-finan kasar Mali darekta Souleymane Cissé ya karbi kyautar Carrosse d'Or, karramawa da aka bashi a birnin Cannes na kasar Faransa lokacin bikin baje kolli da karama masu shirya fina-finan Duniya.Darekta Souleymane Cissé na daga cikin ziratan masu shirya fina-fina a Afrika,wanda tsawon shekaru 50 ya kasance mai fada a ji a wannan masana’anta.