Farfesa Dicko Abdourahmane kan kawo karshen alakar tsaro tsakanin Nijar da Amurka
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:39
Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta sanar da kawo karshen yarjejeniyar tsaro da ke tsakanin kasar da Amurka, tare da zargin cewa dakarun Amurka wadanda adadinsu ya zarta dubu daya na zaune a kasar ne ba a kan ka’ida ba. Sanarwar ta zo ne kwana guda bayan da wata babbar tawagar Amurka ta kamma ziyarar da ta kai Nijar ta tsawon kwanaki uku.
Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Farfesa Dicko Abdourahmane, masani tsaro kuma malami a jami’ar Damagaram Zinder, wanda da farko ya fara yin bayani a game da dalilan da suka sa mahukuntan Nijar suka dauki wannan mataki.
Ku latsa alamar sauti don jin zantawarsu.......
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu