Isa ga babban shafi

Faransa ta rufe ofishin jakadancinta na Nijar har sai abin da hali ya yi

Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta tabbatar da rufe ofishin jakadancinta da ke Yamai a hukumance, matakin da ta ce ta dauka ne har sai abinda hali yayi.

Wata mata a kusa da ofishin jakadancin Faransa da ke Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar. 7 ga Satumba, 2023.
Wata mata a kusa da ofishin jakadancin Faransa da ke Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar. 7 ga Satumba, 2023. © AFP
Talla

Sanarwar ta ranar Talata, ta kara bayyana yadda dangantaka ta yi tsami tsakanin Jamhuriyar Nijar da tsohuwar uwargijiyarta Faransa, lamarin da ya samo asali tun bayan juyin mulkin da  sojoji suka yi wa tsohon shugaba Bazoum Mohamed a watan Yulin shekarar bara.

Cikin sanarwar da ta fitar, ma’aikatar harkokin wajen Faransar ta ce an shafe watanni akalla 5 ana dakile duk wasu ayyukan ofishin jakadancin kasar da ke Nijar, matsalolin da suka hada da hana ma’aikatansu tafiye-tafiye, da kuma hana kai musu ziyara, matakan da suka sabawa yarjejeniyar diflomasiyyar kasashe suka rattaba wa hannu a birnin Vienna, cikin shekarar 1961.

A karshen watan Disamban 2023, Faransa ta fara daukar matakin dakatar da ayyukan ofishin jakadancin nata na Nijar, da bayan dimbin ma'aikatan diflomasiyarta suka fice daga kasar sakamakon tsangwama da neman afka musu da wasu fusatattun mutane suka rika yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.