Isa ga babban shafi

Nijar ta zargi ECOWAS da rashin kyakkyawar manufa akanta

Firaministan Nijar Ali Mahaman Lemine Zeine, ya ce kungiyar kasashe Afirka ta Yamma ECOWAS ko kuma CEDEAO sam ‘’ ba ta kyakkyawar manufa’’ zuwa ga kasar ta Nijar.

Fira Ministan Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine
Fira Ministan Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine REUTERS - STRINGER
Talla

A wannan alhamis ne ya kamata tawagar kungiyar da kuma wakilin Togo da ke matsayin kasa mai shiga tsakani sun kasance a birnin Yamai don tattaunawa da gwamnatin mulkin sojin kasar, amma sai aka wayi gari tawagar ta Ecowas ta kaurace wa taron.

A zantawarsa da manem alabarai a gaban ministan harkokin wajen Togo Robert Dussey, Lemine Zeine ya ce rashin kasancewar tawagar Ecowas a wannan haduwa ta ranar alhamis, alama ce da ke tabbatar wa duniya cewa kungiyar ba ta bukatar tattaunawa, sannan kuma tana rawa ne da bazar wasu kasashe amma ba kare manufofin al’ummar Yankin yammacin Afirka.

A cewar firaministan na Nijar, da farko tawagar Ecowas ta ce ta gaza zuwa Yamai ne saboda jirginta bai samu izinin da ke ba shi damar ratsa sararin samaniya da kuma sauka a kasar ba, zargin da firaministan ya musanta.

Tun ranar 26 ga watan Yulin bara, lokacin da sojoji suka kifar da zababbiyar gwmanati da ke karkashin jagorancin Mohamed Bazoum, kungiyar ta Yammacin Afirka ta sanya wa kasar takunkuman karya tattalin arziki da kuma rufe iyakoki, tare da neman sake dawo da kasar ta Nijar kan turbar dimukuradiyya.

To sai dai yayin da aka gaza samun fahintar juna tsakanin sojojin da suka kwaci mulki karkashin jagorancin Janar Abdourahmane Tchiani da kuma Ecowas, Togo, daya daga cikin kasashe mambobi a kungiyar ta yi gabatar da shirin shiga tsakani wanda bangarorin biyu suka amince da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.