Isa ga babban shafi

Nijar ta dakatar da hulda tsakaninta da kungiyar kasashe rainon Faransa

Sojojin da ke mulkin Jamhuriyar Nijar sun dakatar da dukkanin wata hulda tsakaninsu da kungiyar kasashe rainon Faransa da kuma wadanda suke amfani da harshen Faransanci wato OIF.

Shugaban mulkin sojin Jamhuriyar Nijar Janar AbdurRahmane Tiani tare da mukarrabansa a birnin Yamai.
Shugaban mulkin sojin Jamhuriyar Nijar Janar AbdurRahmane Tiani tare da mukarrabansa a birnin Yamai. REUTERS - STRINGER
Talla

Yayin sanar da daukar matakin, gwamnatin sojin Nijar ta bayyana cewar Faransa ta dade tana amfani da kungiyar ta Francophone Nations wadda ta kunshi kasashe 88, wajen kare muradunta na son kai.

Tun a makon jiya Francophone Nations OIF, ta dakatar da Nijar daga cikinta, gabanin irin matakin da kasar ta dauka a wannan mako.

Matakin Nijar din ya zo ne ‘yan kwanaki bayan da sojojin da suka yi juyin mullki a ranar 26 ga watan Yuli, suka  kammala katse alakarsu da tsohuwar uwargijiyar tasu Faransa, wadda ta taba yi musu mulkin mallaka, ta hanyar korar dukkanin dakarun da a baya kasar ta girke domin taimaka wa yaki da ta’addanci a yankin Sahel.

Babban makasudin kafuwar kungiyar OIFF dai shi ne bunkasa ci gaban harshen Faransanci, samar da zaman lafiya, da kafuwar dimokaradiya, da bunkasa Ilimi, da kuma raya kasashe rainon Faransa.

Sai dai cikin sanarwar baya bayan nan da ta fitar, gwamnatin sojin Nijar, ta bukaci al’ummar  Afirka da su yi watsi da yin biyayya ga ‘yan mulkin mallaka, su kuma koma kishin yada yaruka ko harsunansu, kamar yadda suka gada  daga iyaye da kakanni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.