Isa ga babban shafi

Janar Abdourahamane Tiani ya kai ziyarar farko kasar Mali

Shugaban mulkin sojin Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, a ziyarsa ta farko ya sauka a safiyar yau Alhamis a birnin Bamako, na kasar Mali inda zai gana da takwaransa shugaban mulkin sojan Mali Kanar Assimi Goïta .

Shugaban gwamnatin sojin Nijar Janar Abdorahmane Tianni tare da Kanar Assimi Goita a Mali
Shugaban gwamnatin sojin Nijar Janar Abdorahmane Tianni tare da Kanar Assimi Goita a Mali © Niger Presidency
Talla

 Kasashen Mali da Burkina Faso, karkashin jagorancin sojoji da suka hau karagar mulki ta hanyar juyin mulki a shekarar 2020 da 2022, sun nuna goyon bayansu ga Janar Abdourahamane Tiani wanda ya kwace ikon a Jamhuriyar Nijar karshen watan Yuli.

Burkina Faso,Nijar da Mali sun kama hanyar kirkiro da "Ƙawancen Jihohin Sahel" (AES) wanda zai samar da wani hadin gwiwa ta fuskar  taimakon juna a yayin da ake kai hari kan 'yancin kai da yankunan jihohin uku da kuma ƙarfafa dangantakar tattalin arziki.

Duk da cewa kasashen biyu Nijar da Mali na fuskantar matsin lamba na ƙasa da ƙasa da ke neman komawa kan tsarin mulkin demokraɗiyya, gwamnatocin Nijar da Mali sun haɗa kai a yakin da suke yi da yan ta’ada ko masu ikirarin  jihadi waɗanda hare-harensu ya janyo koma baya a fuskoki da dama na harkokin yau da na kullum a yankin ga baki daya. Shugaba Tiani bayan kasar ta Mali,zai yada zango kasar Burkina Faso,inda zai ganawa da Kyaftin Ibrahim Traore a birnin Ouagadougou.

A wannan ziyarar sada zumunci da aiki Janar Tiani zai  gana da shugaban mulkin sojan Mali, Kanar Assimi Goïta, domin.

Har yanzu dai ba a san tsawon lokacin mika mulki a Nijar ba, amma Janar Tiani ya sanar jim kadan bayan ya dare karagar mulki cewa ba zai wuce shekaru uku ba. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.