Lauyoyin Bazoum sun musanta zargin yunkurin tserewa da ake masa
Lauyoyi hambararren shugaban Jamhuriyar Nijar, sun bukaci a sake shi ba tare da bata lokaci ba, kwana guda bayan sojojin da ke mulkin kasar suka ce sun dakile wani yunkurin tserewa da ya yi tare da iyalansa, kusan watanni 3 bayan daurin talala da aka masa.
Wallafawa ranar:
Ana tsare da Mohamed Bazoum, matarsa da dansa ne ba tare da an bari sun leka waje ko kuma an bari sun gana da lauyoyinsu ba, kamar yadda wata tawagar lauyoyin kasa da kasa da ke wakiltar Bazoum din suka bayyana a wata sanarwa, suna mai musanta zargin yunkurin tserewa da masu juyin mulkin suka ce ya yi.
Hambararren shugaban da mai dakinsa sun kasance karkashin daurin talala ne tun a karshen watan Yuli da aka kifar da gwamnatin farar hula, kuma an yanke musu lantarki da ruwa.
Tun bayan wannan juyin mulkin ne kungiyar ECOWAS/CEDEAO ta shiga takun saka da sojojin da suka kifar da gwamnatin Bazoum na Nijar, lamarin da ya kai ga rufe iyakokin kasar da makwaftanta, har ma Najeriya ta katse mata wutar lantarki.
Zalika, juyin mulkin ya janyo baraka tsakanin Nijar da tsohuwar uwargijiyarta Faransa, inda har sojojnda suka yi juyin mulkin suka sallame jakadanta da dakarun kasar.
Har yanzu dai babu wani ci gaba a game da yunkurin lalubo masalaha a kan wannan dambarwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu