Isa ga babban shafi

Karin farashin kudin kiran waya da na data ya haddasa bore a Nijar

A Jamhuriyyar Nijar hukumar da ke sa ido kan tafiyar da harkokin sadarwa ta kasar ARCEP ta ce ko kadan ba ta da hannu cikin matakin karin kudin sadarwa da kamfanonin sadarwa masu zaman kansu suka yi a ranar lahadin da ta gabata.

Matakin kara kudin kiran wayar dai ya fusata jama'ar Nijar.
Matakin kara kudin kiran wayar dai ya fusata jama'ar Nijar. AP - Vahid Salemi
Talla

Hukumar ta ce kamfanonin sun dau matakin ne bisa rashin fahimtar tsarin da ta yi ne a ranar 31 fa watan Agustan 2022 inda ta kayyade farashi matsakaici da bai kamata su wuce ba.

Hukumar ARCEP ta tabbatar da hakan ne yayin wani taron manema labarai da ta kira a Yamai bayan ganawar da ta yi da kamfanonin sadarwa.

Tuni dai Dalibai suka tsunduma zanga-zanga kan wannan mataki a yau talata don kalubalantar gwamnati ta dauki matakan gaggawa wajen magance matsalar.

Dangane da haka Wakilinmu Baro Arzika ya hada mana rahoto.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.