Isa ga babban shafi

Ana fargabar mutum 4 sun mutu yayin arangamar 'yan Shi'a da 'yan sanda a Kaduna

Akalla mutane hudu ne aka ruwaito sun rasa rayukansu a lokacin da ‘yan sanda suka yi harbin kan mai uwa da wabi domin tarwatsa jerin gwanon motocin mabiya darikar Shi’a a Kadunan Najeriya.

Kungiyar ta kare hakkin dan adam ta ce akalla ‘yan Shi’a 40 jami’an tsaron Najeriya suka hallaka cikin kwanaki 3 da suka yi suna zanga-zanga a Abuja babban birnin kasar.
Kungiyar ta kare hakkin dan adam ta ce akalla ‘yan Shi’a 40 jami’an tsaron Najeriya suka hallaka cikin kwanaki 3 da suka yi suna zanga-zanga a Abuja babban birnin kasar. REUTERS/Abraham Achirga
Talla

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan Shi’ar sun yi dandazo a cikin babban birnin jihar a lokacin da jami’an tsaro musamman ‘yan sandan suka yi yunkurin hana su.

Lamarin dai ya haifar da tashin hankali a tsakanin ‘yan kasar, musamman wadanda ke da sana’o’i da ke kan titin Ahmadu Bello, yayin da ‘yan sanda suka yi ta harbe-harbe don tarwatsa masu zanga-zangar.

Jaridar Dailytrust ta bayyana cewa mutane 20 ne suka jikkata a yayin arangamar da ta auku.

Amma jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar ta Kaduna, ASP Mansir Hasan, ya ce ‘yan sanda uku sun jikkata kuma tuni aka mika su asibiti domin basu kulawar gaggawa.

Ya ce babu wani mabiyin darikar ta Shi’a da aka kashe saboda ba a yi amfani da harsashin gaske ba wajen tarwatsa muzaharar ta su ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.