Isa ga babban shafi

Najeriya: An biya ƙudin fansa kafin sakin ɗaliban Kuriga – Majiya

A Najeriya, yayin da hukumomin kasar ke cewa ba’a biya kudin fansa ba wajen ceto daliban Kuriga na jihar Kaduna, bayanai daga kasar na cewa kungiyoyin ‘yan bindiga uku da ke da hannu a lamarin, sun karbi makudan kadude a matsayin fansa kafin sakin daliban, kamar yadda wasu majiyoyi suka shaidawa jaridar Premium Times da ake wallafawa a kasar.

Yan bindiga a Najeriya
Yan bindiga a Najeriya © Daily Trust
Talla

Aƙalla kungiyoyin ‘yan ta’adda uku da ke aika-aika a jihar Zamfara ne suka yi garkuwa da dalibai sama da 130 a garin Kuriga da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna a kwanakin baya, a cewar majiyoyin.

Daliban sun sami 'yanci ne a ranar Lahadin da ta gabata, makonni biyu da sace su. Tun da farko dai hukumar makarantar ta kiyasta adadinsu ya kai 287, amma daga bisani gwamnan jihar Uba Sani ya ce daliban da aka sace 137 ne, tare da wani malami amma ya mutu a hannun ‘yan ta’addan.

Yello Janbros

Yellow Janbros, daya daga cikin manyan kwamandojin marigayi Ali Kachala ne ya shirya sace mutanen, wanda manazarta suka ce ba shi da wata kwarewa a sace mutane masu yawa.

Daga baya wasu gagararrun ‘yan fashin irin su Dogo Gide da Halilu Sububu suka mara baya. Majiyar jaridar ta ce yayin da wadanda manyan ‘yan bindiga biyu suka taimaka wajen kula da daliban da aka yi garkuwa da su, shi ainihin wanda ya shirya lamarin wato Yellow an bar shi ya fafata da jami’an tsaro da ke kokarin kubutar da daliban.

Rahotanni na cewa sace daliban Kuriga shi ne mafi girma da da Mista Janbros ya jar agama.

"Janbros yana ganin abu ne mai sauki a yi garkuwa da jama'a," in ji wani kwararre kan harkokin tsaro, Yahuza Getso, wanda ya ce ya shiga tattaunawa 84 kuma ya yi nasara a guda daya kachal don sako wadanda aka yi garkuwa da su, kamar yadda ya shaida wa jaridar Premium Times.

Masanin tsaro, wanda shi ne shugaban Kamfanin Eagle Integrated Security and Logistics Ltd da ke Abuja, ya kara da cewa Mista Janbros da tawagarsa sun fuskanci tsaiko daga jami’an soji da ke bin su don ceto daliban da aka sace.”

Sai dai abin takaicin shi ne, an yi nasarar arcewa da daliban lokacin da Dogo Gide da tawagarsa ke fafata da jami’an tsaron.

A cewar Mista Getso

"Duk wata garkuwa da mutane ko tattaunawa ya samu nasara a yankin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, dole sai Dogo Gide ya shiga lamarin"

Yadda aka raba daliban.

Wata majiyar sirrin cikin gida da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar wa Mista Getso cewar, Dogo Gide ya shiga lamarin ne bisa yarjejeniyar za a ba shi wasu daga cikin daliban da aka sace.

Babu hasarar rayuka a bangaren sojoji, amma wasu ‘yan ta’addan da ke taimaka wa Mista Gide wajen yakar jami’an sun rasa rayukansu, a cewar majiyar da ke kusa da Danjibga, wani kauye da ke kusa da dajin Dan Gurgu inda Mista Janbros ya ajiye daliban, kafin ya kai su wajen Sububu a dajin Bawar Daji.

Sojojin Najeriya na sintiri a kusa da Makarantar Firamare da Sakandire ta LEA Kuriga inda aka sace dalibai a Kuriga, Kaduna, Nigeria, ranar 9 ga Maris, 2024.
Sojojin Najeriya na sintiri a kusa da Makarantar Firamare da Sakandire ta LEA Kuriga inda aka sace dalibai a Kuriga, Kaduna, Nigeria, ranar 9 ga Maris, 2024. AP - Sunday Alamba

Ana kyautata zaton Mista Gide ya ji rauni a fadan da ake yi a yayin da rahotanni ke cewa ya mutu.

Majiyar leken asirin ta kara da wani faifan murya da ya tabbatar da inda daliban suke a Bawar Daji.

A cewarsa, an kai dalibai 73 wurin Sububu, inda aka sako wasu matan da aka yi garkuwa da su tun farko daga Dan Gulbi a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara bayan isowar daliban.

Ghana - Most - Go

Kwanaki biyar da sace daliban, wadanda suka sace su sun bukaci a biya su kudin fansa har Naira biliyan daya domin su sako su.

Duk da cewa gwamnatin tarayya ta yi ikirarin cewa sojoji ne suka ceto daliban, sanarwar da gwamnan Kaduna Uba Sani ya fitar na nuni da akasin haka.

Wasu daga cikin daliban Kuriga da suka samu 'yanci a hannun 'yan bindiga.25/03/24
Wasu daga cikin daliban Kuriga da suka samu 'yanci a hannun 'yan bindiga.25/03/24 AP - Chinedu Asadu

Gwamnan, yayin da yake zantawa a gidan Talabijin na Channels, ya ce batun ko an biya kudin fansa ba shi da mahimmanci.

"Abin da ya fi muhimmanci a yau shi ne yaranmu sun dawo gida, Idan aka yi garkuwa da danka, za ku zauna kuna magana kan yadda aka sako shi'?

“A gare ni, abin da ya fi muhimmanci shi ne cewa waɗannan yaran sun dawo gida. Iyayensu suna farin ciki sosai, kuma abin da yake da muhimmanci a gare su shi ne su sake haduwa da ’ya’yansu.

“Amma wasu mutanen da ba su da wata ma’amala da lamarin su ne ke fitowa da wasu ra’ayoyin da ba su dace ba game da ko ana biyan kudin fansa, Abin da ke da muhimmanci a gare mu a Kaduna shi ne yaran sun koma gida.”

Ƙudin fantsa

A wata hira ta wayar tarho da jaridar Premium Times ta samu, wani ganau ya bayyana cewa wasu masu shiga tsakani da ba a san ko su wanene ba ne suka shiga garin Dangabji a cikin motoci kirar Hilux inda suka hadu da wasu kungiyoyin ‘yan bindiga guda biyu wadanda suka bi hanyarsu ta daban bayan karbar kudin fansa da aka shirya a cikin jakunkunan Ghana-Most-Go

"Ni shaida ne, kuma duk mutumin da ke zaune a Kuchere da Danjibga zai iya ba da shaida," ya na shaida wa wani da suke waya da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.