Isa ga babban shafi

Za mu jajirce har sai an yi wa mutanen Tudun-Biri adalci - Sarkin Musulmi

Mai Alfarma Sarkin Musulmi na Najeriya, Muhammad Sa'ad Abubakar ya bukaci a yi adalci ga mutanen da harin sojin kasar ya kashe a garin Tudun-Biri da ke kauyen Karamar Hukumar Igabi ta jihar Kaduna, inda sama da rayuka 100 suka salwanta.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar © Daily Trust
Talla

Sarkin ya fadi haka ne a wurin taron murnar cika shekaru 25 da darewar Sarkin Jama'a Alhaji Muhammad Isa Muhammad kan karagar mulki a fadarsa da ke garin Kafanchan a jihar Kaduna a wannan Juma'ar.

Ba wai kawai taron taya sarki murna ba ne ya kawo mu nan, har da yin addu'a ga masarautar da kuma rayukan mutanen da suka salwanta a Kaduna. Za mu yi matsin lamba don ganin an yi adalci ga mutanen. Inji Sarkin Musulmin.

Wannan na zuwa ne bayan jama'a da dama a Najeriya sun yi ta korafi kan cewa, ba su komai daga bakin Sarkin Musulmin ba tun bayan aukuwar harin na kuskure kan mutanen da ke halartar taron maulidi a garin na Tudun-Biri.

Tuni gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa, lallai za a hukunta duk wanda ke da hannu a wannan harin, inda har mataimakin shugaban kasar, Kashim Shettima ya ziyarci mutanen da ibtila'in ya shafa a asibitin Barau Dikko da ke Kaduna.

Mataimakin shugaban kasar ya sanar da shirin gwamnatin tarayya na sake gina garin na Tudun-Biri da kuma ba su tallafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.