Isa ga babban shafi

Sojojin Najeriya na cacar-baka kan harin bam na Kaduna

Cacar-baka ta barke tsakanin sojojin kasa da na sama na Najeriya bayan harin bam din da ya kashe fararen hula a garin Tudun-Biri da ke jihar Kaduna ta  Najeriya.

Laftanar Janar Taoheed Lagbaja a lokacin da ya ziyarci garin Tudun-Biri da ke Kaduna.
Laftanar Janar Taoheed Lagbaja a lokacin da ya ziyarci garin Tudun-Biri da ke Kaduna. © Nigerian Army
Talla

Wasu kwararan majiyoyi sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa, rundunar sojin sama ta Najeriya ta damu kan yadda rundunar sojin kasa ta tura jirginta mara matuki  da ya yi sanadiyar cilla bam kan masu gudanar da taron maulidi a ranar Lahadi.

Sojojin na kasa ba su yi wata-wata ba wajen amincewa da kuskurensu na kaddamar da farmaki kan masu maulidin, tana mai cewa, ta yi kuskuren kai harin da ta tsara kaddamar da shi kan 'yan ta'adda.

Shugaban sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya ziyarci garin da harin ya auku, inda ya gana da hakimi da malamai da kuma wadanda harin ya rutsa da su, yayin da ya bada tallafin naira miliyan 10 tare da kayayyakin rage radadi.

Laftanar Janar  Taoreed Lagbaja a garin Tudun-Biri bayan harin kuskure kan masu maulidi
Laftanar Janar Taoreed Lagbaja a garin Tudun-Biri bayan harin kuskure kan masu maulidi © Nigerian Army

Sai dai 'yan kwanaki da aukuwar harin, bincike ya nuna cewa, sojojin sama na ci gaba da kumfar-baki kan lamarin.

Daya daga cikin majiyoyin ya shaida wa Daily Trust cewa, yunkurin sojojin kasa mamaye aikin sojin sama, wata alama ce da ke nuna cewa, akwai rashin yarda tsakanin bangarorin biyu.

Wasu daga cikin wadanda harin sojoji bisa kuskure ya shafa a Kaduna.
Wasu daga cikin wadanda harin sojoji bisa kuskure ya shafa a Kaduna. © Daily Trust

Wani sojan sama na kasar ya bayyana cewa, kaddamar da harin sama na bukatar kwarewa da tattara bayanan sirri kafin daukar matakin ragargazar makiya..

Da ma masana sun yi ta korafi kan yadda ake samun rashin jituwa tsakanin sojojin sama da na kasa wajen gudanar da ayyukansu a lokacin yaki da 'yan ta'adda, abin da ke rutsa wa da mutanen da ba su-ji-ba-su-gani ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.