Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun harbe masallata a Kadunan Najeriya

‘Yan bindiga sun kai hari a wani masallaci da ke kauyen Saya-Saya a karamar hukumar Ikara ta jihar Kaduna, inda suka kashe mutum bakwai.

Wani hari da 'yan bindiga suka kai masallancin Juma'a a jihar Kanon Najeriya, wanda ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 120, a watan Nuwamban 2014
Wani hari da 'yan bindiga suka kai masallancin Juma'a a jihar Kanon Najeriya, wanda ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 120, a watan Nuwamban 2014 © Instagram/Aminu Abubakar
Talla

An kashe biyar a cikin masallacin, yayin da sauran biyun aka kashe a wurare daban-daban a yankin.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 8 na dare a lokacin da mutanen kauyen ke yin Sallar Isha’i a wani masallaci da ke yankin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana.

Wani mazaunin kauyen Dan Asabe ya ce an garzaya da wasu mutanen kauyen biyu da suka samu raunukan harbin bindiga zuwa asibiti domin yi musu magani.

Hakimin kauyen Malam Abdulrahaman Yusuf ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce shugaban ‘yan banga na kauyen na cikin wadanda aka kashe a cikin masallacin.

Ya ce jami’an tsaro da suka hada da sojoji da ‘yan sanda daga garin Ikara da kuma yankin Palgore sun isa wurin da misalin karfe 12:30 na safe, amma zuwa lokacin, ‘yan bindigar sun bar kauyen.

A cewarsa, daya daga cikin wadanda suka samu raunukan harbin bindiga an kai shi asibitin Aminu Kano domin yi masa magani.

Mukaddashin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Mansir Alhassan, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an tattara jami’an tsaro zuwa dazuzzukan da ke kusa da su domin zakulo wadanda suka aikata wannan aika-aika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.