Isa ga babban shafi

Najeriya: 'Yan bindiga sun kashe mutum 308 tare da sace 746 a Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna dake Najeriya tace ‘yan bindiga sun hallaka mutane 214 a cikin watanni 3 da suka gabata wajen hare haren da suke kaiwa a cikin jihar, yayin da suka sace mutane 746 suka yi garkuwa da su. 

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai kenan.
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai kenan. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Sanarwar gwamnatin yace daga cikin mutane 214 da ‘yan bindigar suka hallaka tsakanin watan Janairu zuwa Maris na wannan shekara, 14 mata ne, sai kuma maza 196 tare da yara kanana guda 4. 

Kwamishinan tsaron cikin gida Samuel Aruwan da ya gabatar da rahotan yace jami’an tsaro sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga 89 lokacin da suka yi artabu da sojoji da kuma ‘yan sanda a wadannan watanni 3. 

Kwamishinan ya kuma ce wasu ‘yan bindiga guda 5 sun mutu sakamakon fafatawar da suka yi a tsakanin su, abinda ya kawo adadin ‘yan bindigar da suka mutu zuwa 94. 

Gwamnan jihar Malam Nasir El Rufai ya roki gwamnatin tarayya da ta sake mayar da hankali akan yankin arewa maso yamma domin karkade ayyukan ‘yan ta’addan. 

El Rufai yace shirin da sojoji suka kaddamar na zafafa hare hare a karkashin shekarar da ta gabata sun yi matukar tasiri wajen dakile ayyukan ‘yan ta’adda a yankin, inda ya bukaci ci gaba da kai harin har zuwa bayan ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa. 

Gwamnan ya bukaci kai hare haren sama da na kasa a lokaci guda a jihohi 7 dake yankin da kuma yammacin jihar Neja domin kakkabe dazukan da ‘yan ta’addan ke samun mafaka. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.