Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun kashe matar Sarkin Fulani tare da binne gawar ta

‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da mai dakin Sarkin Fulanin  Rugar Ardo Janjala ta karamar hukumar Kagarko a jahar Kaduna da ke Najeriya Abubakar Ardo, sun shaidawa iyalan ta cewa sun kashe tare da binne gawar ta, don haka suyi mata addu’a.  

'Yan bindiga a Tarayyar Najeriya.
'Yan bindiga a Tarayyar Najeriya. © dailytrust
Talla

Daya daga cikin iyalan gidan, Wakili Usman ne ya tabbatarwa jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriya faruwar lamarin, inda ya ce sun kira ‘yan bindigar ne kan su ba su gawar ta, amma jagoran su ya ce sun riga sun jefa ta cikin wani kogo.

Ya ce da dama daga cikin mazauna garin na Janjala musamman mata da yara sun gudu daga cikin sa, sabida yawan garkuwa da mutanen da ake yi a yankin.

Rahotanni sun nuna cewar, ‘yan bindigar sun kashe uwar gidan basaraken Hulaira Abubakar Ardo bayan amsar kudin fansa naira miliyan biyu, amma suka kashe ta sannan suka sako sauran matan sa uku da suka yi garkuwa da su lokaci guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.