Najeriya: 'Yan bindiga sun sace mutane 1,789 a Kaduna cikin watanni 6
Gwamnatin jihar Kaduna dake Najeriya, ta ce adadin mutane da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a jiyar sun kai 1,789 a cikin watanni shida, yayin da jami’an tsaro suka yi nasarar kashe ‘yan bindiga 161 tare da kame da dama daga cikin su cikin watannin.
Wallafawa ranar:
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gidan jihar Kaduna Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da rahoton tsaro, inda yace hare-haren ‘yan bindigar ya kashe fararen hula 285 a tsawon lokacin na watanni shidan yayin da batagarin suka kuma sace shanun da yawansu ya kai 1 da 133.
A cewarsa daga ranar 1 ga watan Yulin da ya gabata zuwa Satumba sai da ‘yan bindigar suka sace mutanen da yawansu ya kai 804 da kaso mai yawa a tsakiyar jihar inda aka saci mutane 508 a lokacin kadai.
Kwamishinan Ya ce an kama mutane 654 da ake zargi a tsawon lokacin da ake binciken.
Barazana ga zabe
A halin da ake ciki, gwamnan jihar Kaduna, Nasir el-Rufai, ya ce tashe tashen hankula a yankin Arewa maso Yamma na da hadari ga zaben 2023 da kidayar jama’a idan ba a magance matsalar ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu