Isa ga babban shafi

Najeriya: 'Yan bindiga sun sace mata mai juna biyu a Kaduna

A Najeriya ‘yan bindiga sun sace wata mata mai juna biyu a unguwar Lema ta yankin Mando  da ke daura da makarantar horar da kananan hafsoshin soji ta NDA da ke Kaduna.

'Yan bindiga na ci gaba da addabar mutane a yankin arewacin Najeriya.
'Yan bindiga na ci gaba da addabar mutane a yankin arewacin Najeriya. The Guardian Nigeria
Talla

‘Yan bindigan sun yi awon gaba da wasu karin mutane 7 a lokacin da suka shiga gidaje 3 da misalin karfe 1 na dare  ranar Lahadi a Mando.

Wasu mazauna unguwar sun ce sun tsorata, saboda haka sun kasa fitowa daga gidajensu a lokacin da suka ji motsin ‘yan bindigan, inda suka yi kira ga gwamnati da ta agaza musu.

Gwamnatin jihar Kaduna ba ta ce uffan a kan lamarin ba, amma kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Mohammed Jalige,  ya ce zai bincika don samun karin bayani a kan abin da ya auku.

Sai dai har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a ji daga gare shi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.