Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun kwace motoci 30 a kan hanyar Birnin Gwari zuwa Funtua

Bayanai daga yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna a Najeriya sun ce, ‘yan bindiga sun tare babbar hanyar da ta tashi daga karamar hukumar ta Birnin Gwari zuwa Funtua, inda suka sace fasinjoji daga motoci akalla 30.

'Yan bindiga a Najeriya.
'Yan bindiga a Najeriya. © Daily Trust
Talla

Kungiyar masu kishin yankin na Birnin Gwari da ake ira da BEPU ta ce a halin yanzu an shafe akalla makwanni uku gungun ‘yan bindiga na tare babbar hanyar da ke sada yankin da garin Funtuwa a jihar Katsina.

Yayin da take bayyana damuwa kan lamarin, kungiyar ta BEPU ta ce yanzu haka motoci da suka hada da manya na daukar kaya 30 ne ‘yan binciga suka kwace.

Kungiyar ta ce ‘yan fashin dajin sun sace dukkanin kayan abinci da sauran na bukatu dake cikin ababen hawan, tare da tilastawa masu motocin biyan kudaden fansar da yawansu ya kama daga naira dubu 300 zuwa miliyan daya kafin karbar dukiyar tasu.

Daga karshe BEPU ta yi karin bayanin cewar an samu saukin hare-haren ‘yan bindiga a kan babbar hanyar da ke sada Birnin Gwari zuwa Kaduna sakamakon matakan tsaurara tsaron da sojojin Najeriya suka yi, sai daii gungun ‘yan bindigar da aka takure a yanzu sun kakarta ta’asar da suke yi zuwa kan hanyar da ta tashi daga yankin zuwa Funtua.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.