Isa ga babban shafi

Najeriya: 'Yan bindiga sun fafata da Ansaru a Birnin-Gwari

Rahotanni daga Najeriya na cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan ‘yan kungiyar ta’addar Ansaru a karamar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna.

Wasu mayakan Ansaru a Najeriya, 24/12/2012.
Wasu mayakan Ansaru a Najeriya, 24/12/2012. AFP PHOTO - JAMA'TU ANSARUL MUSLIMINA FI BILADIS SUDAN
Talla

Rahotanni na cewa ‘yan kungiyar Ansaru na yi wa jama’ar yankin wa’azi ne lokacin da ‘yan bindiga suka bude masu wuta, inda suka kashe mutanen kauyen biyu.

An ce ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen Damari da ke karkashin gundumar Kazage a Gabashin karamar hukumar a kokarinsu na fatattakar mayakan Ansaru   daga kauyen.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda ‘yan ta’addan suka mamaye al’umomin Gabashin karamar hukumar, inda suke jagorantar mutanen kauyukan kan hare-haren ‘yan bindiga.

Fafatawar sa'a daya

Ishaq Usman Kafai, shugaban kungiyar cigaban masarautar Birnin-Gwari (BEPU), wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce an dauki tsawon sa’a guda ana arangama tsakanin kungiyoyin biyu.

A cewarsa, ‘yan kungiyar ta Ansaru wadanda su ma dauke da muggan makamai sun yi galaba a kan ‘yan bindigar wanda hakan ya sanya su (’yan bindiga) suka janye daga kauyen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.