Isa ga babban shafi

Dakarun Najeriya sun kashe kasurgumin dan ta'adda da mabiyansa 30 a Kaduna

Rahotanni daga jihar Kaduna a Najeriya sun ce sojoji sun samu nasarar kashe Ali Dogo, daya daga cikin kasurguman ‘yan ta’addan da suka addabi jama’a da satar mutane.

Wani jirgin yakin rundunar sojin saman Najeriya.
Wani jirgin yakin rundunar sojin saman Najeriya. © The Guardian Nigeria
Talla

Wata majiyar tsaro da ta nemi a sakaya sunanta da kafar watsa labaran PRNigeria ta ruwaito, ta ce an kashe Ali Dogo tare wasu ‘yan ta’addan akalla 30 ne a yayin ruwan wutar da jiragen yakin Najeriya suka yi wa sansanoninsu a wani yanki na karamar hukumar Giwa .

A ‘yan kwanakin baya bayan nan ne dai kasurgumin dan fashin dajin, ya tsere daga maboyarsa da ke jihar Neja zuwa yankin na Giwa a Kaduna, sakamakon hare-hare babu kakkautawa da jiragen yakin suka kaddamar kansa.

Cikin makon da ya gabata, wani rahoton masu bibiyar lamurran tsaro a Najeriya, ya ce an samu raguwar satar mutane a kasar da kashi 28 cikin 100 a watan Agustan da ya gabata na shekarar 2022, idan aka kwatanta da abinda aka gani a cikin watan Yulin da ya gabace shi.

Rahoton ya alakanta raguwar matsalar tsaron da aka samu da hare-haren da sojojin Najeriya tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro suka kaddamar ba kakkautawa kan sansanonin miyagun a sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.