Isa ga babban shafi

'Yan ta'adda sun hallaka wani shugaban al'umma a Kaduna

‘Yan ta’adda sun kai sabon hari a kauyen unguwar Unguwan Liman da ke karamar hukumar Birnin-Gwari a jihar Kaduna, inda suka kashe Mai Unguwar garin tare da yin awon gaba da mutane da dama.

Wasu 'yan bindiga a Najeriya.
Wasu 'yan bindiga a Najeriya. REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo
Talla

Jaridar Punch da ake wallafawa Najeriya ta ruwaito 'yan ta'addan sun kuma yi barazanar sake kai hari garin mai tazarar kilomita uku da hedikwatar karamar hukumar.

Wani mazaunin yankin, Malam Uban Marayu, wanda ya tabbatar da harin a ranar Litinin ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:00 na daren Lahadi a lokacin da ‘yan bindigar suka mamaye garin.

A cewarsa, 'yan ta'addan wadanda suka yi wa kauyen kawanya, sun yi garkuwa da mutane da dama “sun farmaki garin ne da misalign karfe 10:00 na daren jiya.

“Sun kashe Mai Unguwa, sannan su ka yi garkuwa da mutane da ba a tantance adadinsu ba ciki har da mata. A Unguwar Kwanan Shehu da ke kusa da mu, shaguna bakwai kawai suka fasa tare da kwashe kayan ciki”. in ji shi

Kawo yanzu babu wani karin bayani game da harin a hukumance daga gwamnatin Kaduna ko kuma rundinar ‘yan sandan jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.