Isa ga babban shafi

Cutar sankarau ta kashe sama da mutane 20 a jihohi 3 na Najeriya

A Najeriya an samu Karin mutane 23 da suka mutu sakamakon harbuwa da cutar sankarau, tare da 212 da aka tabbatar sun harbu da cutar a cikin jihohi 3 na kasar.

Jihohin Yobe, jigawa da Adaamawa ne aka samu bullar sankarau.
Jihohin Yobe, jigawa da Adaamawa ne aka samu bullar sankarau. AP - Ren Chao
Talla

A wani sabon rahoto da ta fitar a jiya Asabar,  cibiyar yaki da cutuka ta kasar ta ce adadin wadanda suke harbuwa d cutar a duk mako a lokacin da ta yi bincikenta daga 27 ga watan Maris zuwa 2 ga Afrilu sun kai kaso 8.

Rahoton na cibiyar ya nuna cewa jihar Jigaawa a arewa maso yammacin kasar ce ke da kaso 62 na wadanda suka harbu da wannan cuta, a yayin da Yobe da Adamawa a arewa  maso gabashin kasar, inda aka samu mutane 4 da suka harbu da cutar a kowannensu na da kaso 17.

 Cibiyar ta ce daga cikin mutane 23 da suka mutu sakamakon cutar, 17 daga Yobe ne, a yayin da 9 suka mutu a Jigawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.