Isa ga babban shafi

Najeriya ta amince da rigakafin zazzabin cizon sauro

Gwamnatin Najeriya ta amince da sabuwar allurar rigakafin zazzabin cizon sauro daga jami’ar Oxford, inda ta zama kasa ta biyu bayan Ghana a duniya da ta amince da hakan.Alurar rigakafin-R21/Matrix-M, Jami'ar Oxford ce ta haɓaka kuma Cibiyar Serum ta Indiya ta kera.

Cinzon Sauro
Cinzon Sauro © GettyImages/iStock/Christopher Badzioch
Talla

Darakta Janar na Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Najeriya (NAFDAC), Mojisola Adeyeye, ta sanar da ci gaban a yau Litinin a Abuja.

Kamar Ghana, Mojisola Adeyeye ta ce an yi allurar rigakafin cutar zazzabin cizon sauro ga yara daga watanni 5 zuwa watanni 36.

Cizon sauro
Cizon sauro (Photo : US Department of Agriculture/ domaine public)

Ta kara da cewa Najeriya na sa ran samun akalla allurai 100,000 na alluran rigakafin nan ba da dadewa ba kafin amincewar kasuwa ta fara yin wasu shirye-shirye da hukumar kula da lafiya matakin farko ta kasa.

Alurar rigakafin R21/Matrix-M ita ce ta biyu da hukumar ta WHO ta amince da ita kuma ta farko da ta wuce matakin na WHO na kashi 75 cikin dari sama da watanni 12 na bin diddigin.

Alurar riga kafi ta nuna ingancin kariyar kashi 77 cikin 100 na tsawon watanni 12 a cikin gwaji na kashi 2b wanda ya shafi kananan yara a yammacin Afirka, biyo bayan alluran kashi uku na farko.

Alurar rigakafin zazzabin cizon sauro na farko, RTS, S ko mosquirix, daga mai yin magunguna na Birtaniya GSK, Hukumar lafiya ta Duniya ta amince da shi a cikin 2021 bayan shekaru da yawa na aiki. Amma rashin kuɗi ya hana kamfanin samar da allurai masu yawa kamar yadda ake buƙata.

Lokacin da aka amince da maganin sauro, hukumar ta WHO ta ce ta samo asali ne daga sakamakon shirin gwajin da ake yi a kasashen Ghana, Kenya da Malawi wanda ya kai fiye da yara 800,000 tun daga shekarar 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.