Isa ga babban shafi

Birtaniya ta dakatar da daukar ma'aikatan lafiya daga Najeriya

Gwamnatin Birtaniya ta dakatar da hukumomin kasar daga daukar ma’aikatan kiwon lafiya daga Najeriya.

Wasu ma'aikatan kiwon lafiya a Najeriya
Wasu ma'aikatan kiwon lafiya a Najeriya © KOLA SULAIMON/AFP
Talla

Yanzu haka Najeriya ta shiga cikin sahun kasashen duniya da ke fama da gagarumar matsalar karancin ma’aikan lafiya kamar yadda kudnin Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ya nuna.

A cikin watan Maris da ya gabata, WHO ta wallafa wani kundi mai kunshe da sunayen kasashen duniya 55 ciki ha da Najeriya da ke ci gaba da fama da karancin ma’aikatan kiwon lafiya.

Gwamnatin Birtaniya ta ce, ya kamata a bai wa Najeriya da wasu kasashen da ke cikin bakin kundin fifiko wajen bunkasa bangaren kiwon lafiyarsu tare da shata layin da zai hana daukar ma’aikatansu na kiwon lafiya a matakin kasa da kasa.

Da dama daga cikin likitoci da sauran ma’aikatan jinya sun fice daga Najeriya bayan sun samu aiki a kasasahen ketare,inda suke ganin sun fi  samun kulawa a can fiye da kasarsu ta asali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.